IQNA

23:54 - May 03, 2019
Lambar Labari: 3483601
Bangaren kasa da kasa, Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta yi kakkausar suka dangane da siyasar gwamnatin Amurka kan kasar Venezuela.

Kamfanin dillanciuin labaran iqna , kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta soki siyasar kasarta kan shigar shugula  acikin harkokin Venezuela na cikin gida.

Ta ce yanayin da Venezuela take ciki ba yanayi mai kyau ba, kuma siyasar da gwamnatin Amurka ta dauka wajen kara ruruta wutar rikici a kasar ba a bu ne da ya dace ba, maimakon haka hanyar hada kan al’ummar kasar domin warware matsalolinsu ta hanyar tattaunawa ita kadai ce mafita.

A nasa bangaren Mike Pence mataimakin shugaban Amurka, ya zargi Ilhan Omar ta fita tsarin gurguzua  kan tsarin Demukradiya, saboda taki amincewa da siyasar haddasa husuma da rikici da gwamnatin Amurka ta dauka a kan kasar Venezuela.

3808336

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: