IQNA

Ayatollah Khamenei: Sirrin Ci Gaban Al’ummar Iran Shi ne Dogaro Da Kai

19:49 - May 07, 2019
Lambar Labari: 3483614
Jagoran juyin juya halin muslucni a Iran ya gabatar da jawabai dangane da shiga watan azumin ramadana mai alfarma da aka shiga.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya habarta cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a ranar farko ta watan Ramadan a Husainiyar Imam Khomaini, tare da halartar daruruwan jama’a, da kuma jami’an gwamnati daga bangarori daban-daban.

A cikin jawabin nasa jagora ya tabo batutuwa da suke da alaka da siyasa, musamman matsin lambar da kasar take fuskanta daga gwamnatin Amurka ta fuskoki daban-daban, inda ya bayyana cewa wannan matsin lamabar shi ne babban abin da ya kara baiwa kasar damar dogaro da kanta a mafi yawan abubuwan da take bukata.

Haka nan kuma ya yi ishara da muhimmancin mayar da hankali ga ayyukan ibada a cikin watan Ramadan domin samun kusanci da Allah madaukakin sarki, inda ya bayyana wanann wata da cewa shi ne babbar kofa da Allah yake budewa ga bayinsa domin kwararo rahamarsa da gafararsa a gare su.

Inda yana da kyau ga kowane mutum musumi ya yi amfani da wannan damar domin samun wannan babbar falala daga Allah, ta hanyar yin ibada da kuma yin abubuwan da Allah ya yi umarnin da su, da kuma kiyaye wadanda ya yi hani a kansu.

Daga karshe jagoran juyin juya halin musuluncin ya kara jaddada kira ga al’ummar Iran da su zam masu juriya da dogaro da Allah, wanda shi ne babban sirrin cin nasara a kan makiya.

3809444

 

captcha