IQNA

An Yi Gargadi Kan Tiwuwar Kai Hare-Haren Ta’addanci Mami’oi A Ghana

22:37 - May 20, 2019
Lambar Labari: 3483659
Cibiyar bincike kan harkokin tsaro a nahaiyar Afrika ACSIS ta yi gargadi kan cewa, akwa yiwuwar kungiyoyin kasar Ghana ta fuskanci barazanar tsaro daga ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shadin yada laarai na myjoyonline.com ya bayar da rahoton cewa, cibiyar ta ACSIS ta bayar da wani sakamakon binciken da ta gudanar kan kai komon kungiyoyin ‘yan salafiyya masu tsattauran ra’ayi a kasashen yammacin nahiyar Afrika.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan ana samun zirga-zirga ta masu tsattsauran ra’ayi da suke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi a wasu daga cikin kasashen yammacin Afrika.

Rahoton ya ce masu dauke da wannan akidar da suka kaddamar da hare-hare a kasar Burkina Faso a ranar 15 ga Fabrairun 2019, a kan majami’ar mabiya addinin kirista, suna kai koma tsakanin Burkina Faso da Ghana, kuma akwai masu tsatattauran ra’ayi na ‘yan salafiyya da ke tare da wadannan kungiyoyi.

Haka nan kuma raton ya kara da cewa, wadannan mutane suna yin kai komon ne a halin yanzu tsakanin kasar Burkina Faso da Ghana da kuma Togo har zuwa Benin.

3813074

 

 

 

captcha