IQNA

23:50 - June 01, 2019
Lambar Labari: 3483698
Bangaren kasa da kasa, al'ummar Afrika ta kudu sun nuna goyon bayan ga al'umma Palastine sun kuma nemia saka sunan Laila Khaled a wani titi a kasar.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a birane daban-daban na kasar Afrika ta kudu.

A jiya dubban mutanen ne suka gudanar da gagarumin jerin gwanon ranar Quds ta duniya, a mafi mayawan manyan biranan kasar Afrika ta kudu.

Daga biranan da aka gudanar da jerin gwanon da kuma taruka, akwai birnin Johannesbur, birni mafi girmaakasar, sai kuma biranan Pretoria da Cape Town da Durban da dai sauransu.

Masu gudanar da jerin gwanon sun yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin da ya rataya a kansu, an kawo karshendanniyar Isra’ila a kan al’ummar Palastine, kamar yadda suka bukaci gwamnatin kasar da ta rage huldar diflomasiyya da Isra’ila.

Wadanda suka gudanar da wannan jerin gwano dai sun hada da kungiyoyin farar hula, da kuma kungiyoyin muasulmi, gami da wasu ‘yan siyasar kasar, wadanda suke mara baya ga al’ummar Palestine.

 

3816219

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: