IQNA

Putin Ya Yi Kira Da A Rika Karatar Da Yara Littafan Da Aka Saukar Daga Sama

23:54 - June 07, 2019
Lambar Labari: 3483718
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yay i kira da a rika koyar da yara karatun littafan Linjila da kur’ani da kuma Attaura.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da manyan daraktoci na kafafen sadarwa na kasashen duniya a taron da suka gudanar a Rasha, Putin ya bayyana cewa karatar da yara abin da ke cikin littafan Linjila da kur’ani da kuma Attaura yana da matukar muhimmanci.

Putin ya ce idan aka karantar da kananan yara abin da wadannan littafai da aka sakar daga sama suka kunsa, to za a samun canji a duniya ta fukacin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, domin kuw dukkanin wadannan litatfai tushensu dya ne, kuma suna kira ne zuwa ga zaman lafiya da girmama dan adam da ma dukkanin halittun Allah.

Manya daraktoci da ministocin sadarwa na kasashen duniya daban-daban ne suka gudanar da zama a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha, domin samo hanyoyi na kara bunkasa ayyukan sadarwa a duniya.

3817449

http://iqna.ir/fa/news/3817449

 

 

 

 

captcha