IQNA

Za A Gudanar da Zama kan Shirin Iran na nukiliya

22:58 - June 20, 2019
Lambar Labari: 3483755
Kakakin ma'aikatar harakokin kasashen wajen Iran ya sanar da cewa kwamitin hadin gwiwa na kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran zai gudanar da taronsa a birnin Vienna na kasar Austria.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto Sayyid Abbas Musavi mai magana da yanun ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta iran a wannan alhamis na cewa kwamitin hadin gwiwa na kasashen da suka sanya hanu kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da suka hada da ita kanta kasar ta Iran da kuma kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar  zai gudanar da taronsa ranar ashirin da takwas ga wannan wata na Yuni da muke ciki a birnin Vienna fadar milkin kasar Austria.

Kamar yadda aka saba taron dai zai hada mataimakan ministoci  gami da manyan daraktocin siyasa na wadannan kasashe,

Kafin hakan dai kwamitin ya gudanar da irin wannan taro a watan Maris din da ya gabata.

A halin da ake ciki dai jamhoriyar musulinci ta Iran ta fara dakatar da wani bangare na yarjejjeniyar, bayan da kasashen turai suka kasa aiwatar da komai bayan ficewar kasar Amurka daga yarjejeniyar wadda ayi shekara guda da ta gabata.

Haka nan Iran ta baiwa kasashen Turan wa'adin watanni biyu na daukan matakin kare yarjejeniyar ko kuma ta dauki wani mataki na gaba, a halin da ake cikin yanzu, kasa da wata guda  ya rage wa kasashen Turan na wa'adin da kasar Iran ta ba su.

 

 

 

3820984

 

 

captcha