IQNA

kungiyoyi da Cibiyoyi 75 Sun Yi Watsi Da Yarjejeniyar Karni

23:51 - June 26, 2019
Lambar Labari: 3483774
Kungiyoyi da cibiyoyi guda 75 a kasashe daban-daban na nahiyar turai sun fitar da bayani na hadin gwiwa da ke yin tir da Allawadai da shirin yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Talata kungiyoyi da cibiyoyi 75 ne daga kasashe daban-daban na nahiyar turai, da suka hada da kungiyoyin lauyoyi da masu raji kare hakkokin dan adam, har ma da wasu bangarori na ‘yan siyasa, suka fitar da bayani na hadin gwiwa, wanda a cikinsa suka yi watsi da yarjejeniyar karni.

Bayanin wanda aka fitar a kasashe daban-daban da suka hada da Jamus, Girka, Italiya, Holland Birtaniya, Danmark da sauransu, ya yi tir da Allawadai da hankoron sayar da Falastinu ga Isra’ila da sunan yarjejeniyar karni.

Wannan na zuwa neadaidai lokacin da aka fara gudanar da taron tattalin arziki da saka hannayen jari a Falastinu, wanda Amurka ta shirya da nufin bunkasa harkokin tatalin arzikin falastinawa.

A lokacin bude zaman taron a jiya a birnin Manama na kasar Bahrain, Jared Kushner mahawarcin Trump kan harkokin gabas ta tsakiya kuma surukinsa, wanda shi ne ke jagorantar taron, ya bayyana cewa a cikin shirin nasu babu batun kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta, amma za a bunkasa tatalin arzikin falastinawa a karkashin daular yahudawan Isra’ila.

3822326

 

captcha