IQNA

Rouhani: Dole A Warware Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Ta Hanyar Tattaunawa

23:45 - July 23, 2019
Lambar Labari: 3483871
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Iran Hojjatol Islam Hassan Rauhani ya bayyana alaka tsakanin kasashen Iran da Iraki da cewa alaka ce ta tarihi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaba Rauhani ya bayyana hakan neadaren jiya a lokacin da yake ganawa da Firayi ministan kasar Iraki Adel Abdulmahdi, wanda yake gudanar da ziyarar aiki a Tehran.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma wajabcin hanzarta aiwatar da yarjeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a lokutan baya tsakanin Iran da Iraki abangarori daban-daban.

Rauhani ya ce a cikin shekarun baya-bayan nan alaka tsakanin Iran da Iraki ta yi karfin da ke tabbatar da cewa alaka ce ta tarihi, wadda za a ta ci gaba da bunkasa domin amfanin al’ummomin kasashen biyu.

Dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya a cikin ‘yan kwanakin nan kuwa, Rauhani ya jaddada cewa Iran ba za ta taba shiga yaki da wata kasa ba, har sai idan an tsokane ta ne, alokacin za ta kare kanta.

A nasa bangaren firayi ministan kasar ta Iraki Adel Abdulmahdi ya yaba da irin rawar da kasar ta Iran take takawa wajen habbaka ci gaban kasar Iraki a bangarori na ci gaban ilimin kimiyya da fasaha, da kuma bunkasar masana’antu.

Haka nan kuma firayi ministan kasar ta Iraki ya ce, kasarsa ba za ta taba zama daga cikin kasashen da za su aiwatar da takunkumin tattalin arziki na wata kasa a kan kasar Iran ba.

Yanzu haka dai kasar Iraki na a matsayin kasa ta farko a duniya da ake sayar da kayan masarufi da Iran take samarwa, kamar yadda wasu daga cikin yankunan kasar ta Iraki suna samun wutar lantarki da iskar gas ne kai tsaye daga kasar ta Iran.

 

3829264

 

 

captcha