IQNA

An Fara Rusa Gidajen Falastinawa A Kauyen Sur Baher

23:48 - July 23, 2019
Lambar Labari: 3483872
Bangaren kasa da kasa, Isra’ila ta fara aiwatar da shirinta na rusa gidajen falastina a kauyen Sur Baher da ke kusa da birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Isra’ila ta fara rusa gidajen falastinawa a cikin kauyen Sur Baher da ke gabashin birnin Quds, ta hanyar yin amfani da manyan motocin buldoza wajen aiwatar da shirin.

Rahoton ya ce jami’an tsaron Isra’ila ne dauke da makamai suke bayar da kariya domin aiwatar da shirin, inda daruruwan falastinawa suka yi curko-curko a waje suna kallon ana rusa gidajensu, ba tare da sun isa su ce uffan ba.

Tun kafin wannan lokacin dai firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sa sanar da cewa gwamnatinsa za ta fara aiwatar da wanann shiri na rusa gidajen falastinawa a a kauyen Sur Baher, bisa hujjar cewa an gina gidajen ne ba bisa ka’ida ba, inda Isra’ila take da niyyar gina wasu sabbin matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna a inda aka rusa gidajen falastinawan.

Wanann shiri dai na shan kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya, da hakan ya hada har kwamitin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya, amma Isra’ila tana ci gaba da yin kunnen uwar shegu da wadannan kiraye-kiraye.

.

3828988

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha