IQNA

An Girmama Karamar Yariya Mahardaciya Kur’ani A UAE

23:52 - August 08, 2019
Lambar Labari: 3483927
Bangaren kasa da kasa, an girmama yarinya mafi karancin shekaru da ta hardace kur’ani a  UAE.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Al’ain cewa, Reim Abdallah Alfalasi bababr daraktar cibiyar kula da kananan yara ta kasar haddaiyar daular larabawa, ta girmama yarinya mafi karancin shekaru da ta hardace kur’ani a kasar.

Ta ce samun kananan yara mahardata kur’ani a cikin kasa babbar rahama ce ta ubangiji, a kan girmama irin wadannan yara da mahaifansu ya zama wajibi.

Misam yahya Muhammad ita ce yarinya mafi karancin shekaru da ta hardace kur’ani a kasar hadaddiyar daular larabawa.

A halin yanzu tana da shekaru 6 da haihuwa, kuma ta samu nasarar hardace kur’ani mai tsarki.

 

3833465

 

captcha