IQNA

Palestine Ce Limaman Juma’a Suka Huduba A Kanta A Turai

23:54 - August 09, 2019
Lambar Labari: 3483930
Bangaren kasa da kasa, limaman juma’a a masallatai a na kasashen turai sun mayar da hankali kan batun Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin maa cewa, a yau limaman juma’a a masallatai a na kasashen turai daban-daban sun mayar da hankali a cikin hudubobinsu a kan batun Falastinu da kuma halin da take ciki.

Abu Karim Farhud shugaban kwamitin taimakon al’ummar falastinua  kasashen turai ya bayyana cewa, a cikin hudubobin juma’ar yau, limamai a kasashen turai sun I magana kan halin da ae cikia  Falastinu.

Ya ce ci gaba da kara matsa lamba da yahudawa key i wajen rusa gidajen falastinawa da korarasu daga yankunansu, shi ne babban abin da yafi daga hankula a wannan lokaci.

Ya kara da cewa akwai bukatar musulmi su hada karfi wuri guda domin tunkarar wannan barazana da ke neman shafe yan uwansu falastinawa daga samuwa.

3833616

 

 

captcha