A gobe Lahadi ne mahajjatan za su yi jifar shaidan na biyu, sannan kuma su kasance a Mina har zuwa marecen ranar Talata bayan jifar shaidan karo na uku za su kammala ayyukansu na hajji, inda za su koma Makka, inda daga nan ne kuma za a fara shirye-shiryen komawa gida.
Aikin Hajji dai nadaya daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da yake a matsayin wajibi a kan kowane musulmi mai hali.
Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga watan Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.
A kowace shekara miliyoyin musulmi ne daga kasasheh duniya daban-daban ke gudanar da aikin Hajji abirnin Makka mai alfarma.