IQNA

An Bude Masallaci Mafi Girma A Turai A Chechniya

23:56 - August 23, 2019
Lambar Labari: 3483978
Bangaren kasa da kasa, an bude masallaci mafi girma anahiyar turai baki daya agarin Chali na Cechniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na jo2.met cewa, a yau bude masallaci mafi girma anahiyar turai baki daya, wanda Ramadan Qadirov shugaban jamhuriyar Chechinuya ya jagoranci budewa, wanda kuma aka bashi sunan Iftikharul Muslimin.

An yi amfani fasaha ta zamani wajen ginin masallacin, wanda bakasafai akan samu irinsa a hatta a cikin kasashen musulmi da dama ba.

Yana da fadin ita murabba'i 9700, kamar yadda kuma masallata dubu 20 za su yi yin salla a cikin ginin masallacin a lokaci guda, kamr yadda kuma mutane dubu 100 za su iya yin salla a cikin harabarsa.

 

3836866

 

 

captcha