IQNA

Shekaru 6 Cibiyar Kur’ani ta “Isra” Tana Gudanar Da Ayyukanta A Afghanistan

23:15 - September 13, 2019
Lambar Labari: 3484045
Bangaren kasa d kasa, cibiyar Darul Kur’ani ta Isra ta kwashe shekaru 6 tana gudanar da ayyukanta a Afghanistan.

Abdulshakur Fallah malami a wannan makaranta a zantawarsa da IQNA ya bayyana cewa, wannan cibiya an kafa ne tun shekaru shida da ska gabata, kuma Sheikh Ahmad Ali dan kasar Masar ne ya kafa ta a shekara ta 2013, kuma tana gudanar da ayyukanta ba tare da mutane da dama sun sani ba.

Ya ce babbar manufar wannan makarantar kur’ani dai ita ce samar da wata hanya ta tarbiyantar da matasa kan sanin kur’ani d akuma karatunsa, da kuma ganin cewa tasirin kur’ani ya shiga cikin zukatansu.

Haka nan kuma dangane da karbuwar makarantar ya bayyana cewa, makarantar ba ta taba yin talla kan ayyukanta ba, mutane suke kawo yaransu da kansu, domin kuwa ko allo babu da sunan makarantara a kanka allo a kan gininta.

Ya ce babban abin farin ciki shi ne, yadda iyayen yara suke nuna gamsuwa da yadda makarantar take koyar da ‘ya’yansu karatu da hardar kur’ani mai tsarki.

Ya kara da cewa daya daga cikin dalilan da suka sanya aka boye sunan makarantar da kuma rashin shi ne, domin kaucewa hare-haren  mayakan Taliban masu dauke akidun kafirta musulmi.

3841436

 

 

captcha