IQNA

Taron Karfafa 'Yan Uwantakar Musulunci A Masar

23:59 - September 18, 2019
Lambar Labari: 3484063
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron karawa juna sani kan karfafa yan uwantakar uslunci a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, reshen jami’ar Azahar a birnin Iskandariyya ya sanar da cewa, ana shirin gudanar da wani babban taron karawa juna sani na kasa da kasa, kan karfafa ‘yan uwantak a musulunci.

Wanann taron wanda shi ne irinsa na farko da cibiyar za ta dauki nauyin gudanarwa, wanda zai samu halartar masana da malamai daga kasashen duniya daban-daban.

Babbar manufar taron dai itace kara fito da matsayin ‘yan uwantak da ufin karfafa al’ummar musulmi, wamda rashin hakan ne ya zama daya daga cikin dalilan da suka raunana musulmi a  halin yanzu, ta yadda ba su da karfin fada a ji duniya.

Jami’ar azahar ce dai za ta dauki nauyin taron tare da ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar masar, inda ake sa ran taron zai samu halartar manyan jami’an gwamnatin Masar da kuma na wasu kasashen musulmi.

 

3843099

 

 

 

captcha