IQNA

Trump Ya Ce Zai Tsananta Takunkumai Kan Iran

20:34 - September 19, 2019
Lambar Labari: 3484067
Bangaren kasa da kasa, Trump ya bayar da umarnin kara tsananta takunkumai a kan Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, yayin da yake ganawa da sabon babban mai bayar da shawara kan harakokin tsaro na kasar Amurka, Shugaba Trump ya bayyana cewa cikin sa'o'i arbain da takwas masu zuwa za a bayyana sabin takunkumin da a kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi ikrarin cewa zai kara kakabawa kasar Iran din sabin takunkumi na karya tattalin Arziki.

A safiyar jiya laraba ne shugaban na Amurka ya rubuta a shafinsa na twitter cewa ya bawa saktaren harakokin kudin kasar umarnin sake kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran takunkumi.

Masana na ganin cewa manufar Amurka na sake kakabawa kasar Iran din takunkumi shi ne karin matsin lamba ga kasar ta yadda za ta bi manufofin kasar Amurka, abinda hukumomin birnin Tehran suka bayyana a matsayin marasa tasiri, kuma har abada Amurka ba za ta cimma wannan manufa ba.

Kashin da kawayen Amurka ke sha a yankin, kama daga haramtacciyar kasar Isra'ila daga hanun kungoyoyin gwagwarmaya da kuma 'yan ta'addar ISIS, ga kuma harin da dakarun tsaron kasar Yemen suka kai kan ciboyoyin sarrafa man fetir na kasar Saudiya na daga cikin batutuwan da suka kara harzika Amurka kan sake kakabawa kasar Iran din takunkumi.

3843217

 

 

 

 

 

 

 

captcha