IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Ashura Da Kur’ani A Kasar Mali

22:26 - September 22, 2019
Lambar Labari: 3484076
An gudanar da zaman taron karawa juna sani mai taken Ashura da kur’ani a birnin Bamako na kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, a jiya an gudanar da zaman taron karawa juna sani mai taken Ashura da kur’ani a birnin Bamako na kasar Mali tare da halartar masana.

Sheikh Dawud Jakti babban malamin addini kuma wakilin hubbaren Hussaini a Mali shi ne ya jagoranci gudanar da taron.

Fiye da masana 50 e suka halarci zaman taron, gami da daliban jami’a matasa maza da mata.

Haka nan kuma taron ya mayar da hankali ne kan matsayin ahlul bait (AS) da kuma muhimman darussan da suke a cikin waki’ar Ashura, kamar yadda masana suka gabatar da kasidu kan wannan maudu’i, tare da yanin ayoyin kur’ani da ke magana kan sadaukarwa, tare da bayyana yadda Imam Hussain (AS) ya aikata hakan a aikace.

Sheikh Jakti a karshen taron ya bayar da kyautuka da cibiyar kula da hubbaren Hussani ta bayar domin rabawa.

 

3843720

 

 

 

 

captcha