IQNA

Hizbulah Ta Caccaki Zaman Taron Kasashen Larabawa

23:25 - April 02, 2019
Lambar Labari: 3483509
Kungiyar Hizbullaha kasar Lebanon ta yi kakkausar suka dangane da abubuwan da bayanin bayan taron shugabannin kasashen larabawa ya kunsa.

kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa,a  cikin bayanin da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya, ta bayyana abin da ke kunshe a  cikin bayanin bayan taron shugabannin kasashen larabawa da cewa babban abin kunya ne.

Bayanin na kungiyar Hizbullah ya bayyana yadda kasashen larabawan suka nuna gazawa a fili wajen kasa yin Allawadai da matakain da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qods a matsayin fadar mulkin Isra'ila, da kuma matakin baya-bayan na ayyana tuddan Golan na Syria a matsayin mallakin Israla.

Kungiyar ta Hizbullah ta ce abin da shugabannin kasashen larabawa suka yi ba suna wakiltar al'ummomin larabawa ba ne, suna wakiltar kansu da kujerunsu na mulki da sarauta, domin kuwa al'ummomin larabawa ba su amince da mika Palastinu da yahudawan Isra'ila ba, kamar yadda ba za su ta amincewa da mika wani yanki na kasar Syria ga yahudawa ba.

 

3800671

 

captcha