IQNA

An Kafa Wani Kwamitin Mabiya Addininan Musulunci Da Kirista tsakanin Vatican da Azhar

10:11 - March 19, 2014
Lambar Labari: 1388821
Bangaren kasa da kasa, an kafa wani bababn kwamiti wanda ya hada musulmi da kuma mabiya addiin kirista wanda babbar majami’ar katolika ta ta Vatican da cbiyar Musulunci ta Azahar suka jagoranci kafawa da nufin kara kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinan biyu.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rtl cewa an kafa wani bababn kwamiti wanda ya hada musulmi da kuma mabiya addiin kirista wanda babbar majami’ar katolika ta  Vatican da cbiyar Musulunci ta Azahar suka jagoranci kafawa bayan rattaba hannu tsakanin wakilansu.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar hakan ita ce samar da wani yanayi na zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin biyu a dukkanin fadin duniya, tare da yaki da duk wani lamari da ke da alaka da neman haddas fitina tsakanin su ko kyama, kuma shirin zai ci gaba da gudana har zuwa shekara ta 2020, kamar yadda kuma zai iya hadawa har da wasu sauran addinan ian suna da bukatar shiga cikinsa.
A yayin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya dai an samu halartar wakilan babbar cibiyar ta Musulunci ta Azhar, da kuma manyan limaman babbar majami’ar gami da wakilan wasu majami’on daga kasashen turai, gami da kasar Australia, lamarin da ya samu karbuwa tare da yin lale marhabin da shi daga dukaknin bangarori.
1388488

Abubuwan Da Ya Shafa: vatican azhar
captcha