IQNA

Yin Amfani Da Mahangar Ayatollah Khamenei Zai Taimaka Wajen Warware Matsalolin Al’umma

19:48 - April 30, 2011
Lambar Labari: 2114726
Bangaren kasa da kasa, yin amfani da mahangar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zai taimaka matuka wajen warware da dama daga cikin matsalolin da suka addabi al’umma a wannan zamani, bisa la’akari da yadda yake hangen lamurra da kuma warrware su ta mahanga mai zurfi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya yi da shugaban jam’iyar nan ta Hizb Tauhid a kasar Lebanon Wiam Wahhab ya bayyana cewa, yin amfani da mahangar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zai taimaka matuka wajen warware da dama daga cikin matsalolin da suka addabi al’umma a wannan zamani, bisa la’akari da yadda yake hangen lamurra da kuma warrware su ta mahanga mai zurfi, wanda kuma a cewarsa hakan zai yi amfani ga dukkanin bangarori na musulmi, da ma wadanda ba musulmi ba.
A bangare guda kuma wani labari da iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na associated Press an bayyana cewa, sakamakon wani jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Masar ya yi nuni da cewa akasarin al’ummar kasar na bukatar ganin an fitar da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulki daga kur’ani mai tsarki, maimakon irin tsarin da ya gabata wanda babu ruwansa da addinin muslunci a dukkanin lamurransa.
Da dama daga cikin wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun bayyana cewa su dai musulmi ne, kuma wajibi ne dokokin kasarsu su yi daidai da koyarwar addininsu, ba tare da kuma an takura wani bangare ba, ta yadda za aiya baiwa kowa hakkinsa kamar yadda ya kamata amatsayinsa na dan kansa, kuma sun yi imanin cewa dokokinsu za su dace da musulunci kasantuwarsu musulmi.
782963

captcha