IQNA

Amnesty International Ta Suka Kan Rusa Babbar Jam’iyyar Siyasa A Bahrain

13:53 - September 25, 2016
Lambar Labari: 3480804
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty International ta yi Allawadai da kakkausar murya dagane da rusa jam’iyyar Alwifaq da mahukuntan Bahrain suka yi.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin press TV cewa Philip Lotter babban darakta mai kula da harkokin kungiyar a bangaren shari’a, ya bayyana matain na mahukuntan kasar Bahrain da cewa ya yi hannun riga da dukkanin lamurra da suka danganci doka.

Ya kara da cewa tun bayan da masarautar kasar ta fara daukar matakan ganin bayan jam’iyyun adawa kungiyoyin kae hakkin bil adama na duniya suke nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki, amma kuma babu wani au a aikace daga bangaren mahukuntan.

Haka nan kuma yi ishara da irin goyon bayan da wannan masarata take samu daga manyan kasashen duniya wajen ci gaba da murkushe yan siyasa akasar shi ne babban abin da ke kara mata karfin gwiwa wajen daukar irin wadannan matakai na kama karya.

Ya ce a halin yanzu mahukuntan Bahrain sun hana dukkanin bangarori na kasa da kasa gudanar da duk wani bincike kan lamarin ta hanyar hana su izinin shiga kasar, balantana a bi lamarin ta hanyar bincike domin tabbatar da cewa an daidaita a tsakaninsu.

Tun a cikin shekarar 2001 ce dai jam’iyyar Alwifaq ta mabiya mazhabar shia’ wadada su ne masu rinjaye a kasar ta Bahrain ta shiga zabe, ta kuma lashe dukkanin kujerun majalisar 18 baki daya, lamarin da ya saka firgici a cikin zukatan mahukuntan kasar.

Al’ummar Bahrain dai taki mika wuya ga salon zalunci da mulkin kama karya na masarautar kasar da ke neman ya mayar da mutanen kasar tamkar bayi a lokacin mulkin jahiliyyar larabawa bayan shudewar fiye da shekaru dubu da kawo karshen irin wannan salon a mulkin zalunci.

Daga karshe jami’in ya yi kira ga dukkanin bangarori na duniya da suka hada da gwamnatoci masu ‘yancin siasa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama da su mike domin takawa mahukuntan Bahrain birki kan wannan bakin zalunci da suke yi kan yan siyasa masu mas adawa.

3532295


captcha