IQNA

An Gudanar Da Taron Arbaeen na Imam Hussain (AS) tare da Halartar Jagora

22:42 - November 20, 2016
Lambar Labari: 3480956
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron arbaeen na Imam Hussain (AS) a Husainiyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagoran juyin Islama da kuam daruruwan malamai da dalibai.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan zaman makokin arbaeen na Imam Hussain (AS) ne a yau, a Husainiyar Iamm khomeni (RA) wanda mutaen da dama suka samu halarta.

Hojjatol Islam Panaheyan ne ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana muhimman lamurra da suka shafi wannan yunkuri da sadaukantarwa ta Imam Hussain (AS) da kuma hikimar da ke tatatre da hakan, gami da irin darussan da ya kamata al'ummar msuulmi su dauka dangane da hakan, musamman ma mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.

To daya bangaren kuma kakakin komitin kula da makokin arba'een a nan Iran ya ce masu ziyara daga kasashen waje kimani miliyon guda ne suka shigo kasar don gudanar da makokin arba'in na Imam Husain (as) a cikin kasar.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Hamid Riza Gudarzee kakakin kimitin arba'in na immam husain (a) yana fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa masu ziyarrar sun shigo ne ta kan iyakoki hudu na kasar wadanda suka hada da tashoshin jiragen sama na kasa da kasa.

3547362


captcha