IQNA

Wata Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta Bukaci A Saki Sheikh Zakzaky

21:08 - December 27, 2016
Lambar Labari: 3481073
Bangaren kasa da kasa, wata kungiyar kare hakkin bil adama Najeriya ta bukaci a saki sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi ba tare da wata tuhuma ba.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya nakalto daga jaridar The Nation da ake bugawa a Najeriya cewa, wata kungiyar farar hula a kasar ta bukaci mahukunta da su girmama umarnin da kotun tarayya ta bayar da ke neman a saki Sheikh zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

Bayanin kungiyar ya ce rashin sakin malamin wata manuniya ce a kan yadda doka bata aiki a Najeriya, kuma alamu ne da ke nuni da cewa an kama hanyar kama karya Kenan maimakon mulkin dimokradiya wanda al'umma suka zabi gwamnati dominsa.

Bayanin ya ce duk da cewa gwamnatin Kaduna da kanta ta tabbatar da kasha daruruwan magoya bayan malamin da sojoji suka yi a gidan malamin a lokacin da suka kame shi, amma har yanzu ba hukunta koda wani jami'in soji guda kan hakan ba.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Amnesty International ta jadda kiranta ga mahukuntan Najeriya da su saki malamin, kuma a hkunta duk wanda yake da hannu a kisan gilar da aka yi wa mabiyansa.

3556994


captcha