IQNA

Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allah wadai Da Harin London

23:39 - June 04, 2017
Lambar Labari: 3481580
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Birtaniya ta yi tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a birnin London fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar a jiya, ta yi Allah wadai da kakakusar murya da wannan aiki wanda ta bayyana shi da cewa na ta’addanci ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa, musulmin kasar Birtaniya suna taya dukkanin iyalan wadanda abin ya rutsa da su alhin abin da ya faru, tare da bayyana wadanda suka kai harin da cewa mutane masu kesassar zuciya, kuma abin da suka yi ba shi da wata dangantaka da wani addini.

Haka nan kuma bayanin majlaisar musulmin kasar ta Birtaniya ya yi ishara da cewa, duk wanda yake aikata ta’addanci da kisan bil adama da cusa tsoro a cikin zukatan jama’a da sunan wani addini da aka saukar daga sama, to hakika baya biyayya ga koyarwar wannan addinin.

A cikin daren Asabar da ta gabata ce aka kai harin na birnin London, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 da kuma maharani su uku.

3606415


captcha