IQNA

Majami’ar London Ta Dauki Nauyin Shirya Buda Baki

23:55 - June 08, 2017
Lambar Labari: 3481591
Bangaren kasa da kasa, a wani mataki na mayar da martani ga ‘yan ta’adda kan harin da suka kai a birnin London, musulmi da kiristoci sun gudanar da buda baki tare.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bexleytime ya bayar da rahoton cewa, majami’ar mabiya addinin kirista ta Saint Mary da ke London, ta shirya gudanar da buda baki na bai daya tare da halartar musulmi da kuma kiristoci.

Sarkan Standak daya ne daga cikin mambobin majalisar musulmin Birtaniya ya bayyana cewa, shirya wannan buda baki da wannan babbar majami’a ta yi yana a matsayin mayar da martani ga ‘yan ta’adda da suka kai hari a London da sauran yankuna na Birtaniya, da su san cewa ba za su iya raba kan al’ummar kasar ba.

Ya kara da cewa, a kowane lokaci musulmi suna yin kira ga sauran mabiya addinai da su san cewa abin da ‘yan ta’adda suke yi ba musulunci ba ne, domin kuwa muslunci yana kira ne zuwa ga zaman lafiya, kuma wannan majami’a da ta shirya buda baki da ya hada musulmi da kiristoci, ya kara tabbatar da cewa musulmi musulmi da kiristoci suna zaune lafiya tare da girmama juna.

Harin da ‘yan ta’adda suka kai a ranar Lahadi da ta gabata a birnin London, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 tare da jikkatar wasu 47 na daban.

3607386


captcha