Ta kara da cewa 'yan ta'addan da suka kai hare-haren London ba suna wakiltar musulmi ba ne, saboda haka babu dalilin da zai sanya a kyamci musulmi, domin manufar 'yan ta'adda ita ce raba al'umma da suke zaune lafiya da juna.
A lokacin da take maganada musulmi ta yi kira da cewa, a duk lokacin da musulmi suka ga wani a cikinsu da suke da tabbacin yana da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda ko kuma suke zarginsa da hakan, su gaggauta sanar da 'yan sanda, domin sai da hadin kan musulmi ne za a samu damar zakulo 'yan ta'adda da suke fakewa da sunan addinin suna aikata ta'addanci.
Cressida Dick ta kara da cewa, tun bayan harin London da aka kai 'yan kwanakin da suka gabata, kyamar da ake nunwa musulmi ta rubanya kusan sau biyar, abin da rundunar 'yan sandan London bat aba amince da shi ba.