IQNA

An Cinna Gobara Da Gangan A Kan wani Gini na Musulmi A London

23:52 - June 14, 2017
Lambar Labari: 3481610
Bangaren kasa da kasa, wani gini mai hawa 24 ya kama da wuta a birnin London na kasar Birtaniya wanda musulmi suke zaune a cikinsa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga tashar rt cewa, Wata mumunar gobara cikin daren Talata a London, ta mamaye wani bene mai hawa 24 dauke da gidaje masu yawa da ya zuwa yanzu, ba a tantance musabbabinta ba. Tuni dai hukumomi suka bayyana lamarin da wani babban bala'i.

Akalla jami'an kwana-kwana dari biyu ke kokarin shawo kan gobarar da ta kama wani dogon benen mai hawa 24 da ke yammacin birnin na Londoninda mutane da dama suke rayuwa.

Gobarar ta fara ne kusan karfe daya na dare agogon kasar ta kuma mamaye ilahirin katafaren ginin ne inda mutane da dama ke barci a cikinsa. Ko a safiyar wannan Larabar ma dai wasu hotuna sun kwada irin ta'asar da wutar ke yi.

Shaidu sun ce sun yi ta jin yadda mutane ke kururuwar kiran kai masu dauki cikin ginin wanda ke dauke da gidaje dari da ashiriin da daya.

An dai yi nasarar ceto mutane, sannan kuma an yiwa wasu kimanin talatin maganin a wasu asibitoci.

Wutar wadda ta kazanta matuka, ka iya lakume kafatanin ginin da ke a North Kensington da ke a yammacin birnin na London.

3609687


captcha