IQNA

Jeremy Corbin: Ba Za Mu Yarda Da Gallza Wa Duk Wani Musulmi Ba

17:17 - July 05, 2017
Lambar Labari: 3481672
Bangaren kasa da kasa, Shugaban jam'iyyar Labour a kasar Birtaniya Jeremy Corbin ya bayyana cewa, ba za su taba maincewa da gallaza wa musulmi ba da sunan fada da 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jaridar Guardian ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da cika makonni biyu da kai hari a kan wani masallaci a kasar Birtaniya, , shugaban jam'iyyar Labour a kasar Jeremy Corbin ya bayyana cewa, babu wani dalilin da zai sanya a dauki karan tsana a dora kan musulmi, wannan yana a matsayin nuna wariya ne ga wani bangaren al'umma.

Jeremy Corbin ya ce, kamar yadda ba su yarda da ta'addanci ba kuma suke yin Allah wadai da masu aikata shi, haka kuma suke yin Allah wadai da masu nuna kyama ga musulmi.

Ya ce rashin adalci ne a dora laifin ayyukan ta'addanci a kan dukkanin msuulmi, domin kuwa masu aikata ta'ddanci ba suna yin hakan ba ne da yawun dukaknin msuulmi, bil hasali mafi yawan musulmi a duniya ba su amince da hakan ba, suna ma yin Allah wadai da hakan.

Daga karshe ya yi kira ga dukkanin al'ummar Birtaniya da su ci gaba da yin zaman lafiya tare da musulmi, tare da bayar da tabbacin cewa musulmi a shirye suke su bayar da tasu gudunmawa domin murkushe 'yan ta'adda a duk inda suke.

3615684


captcha