IQNA

Nuna Abincin Halal A Birnin Toronto Na Kasar Canada

23:55 - July 06, 2017
Lambar Labari: 3481675
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani baje kolin kayan abincin halal mafi girma yankin arewacin Amurka a birnin Toronto na kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Radio Canada International cewa, wannan taron baje kolin kayan abincin Halal shi ne karo na biyar da za a gudanar da shi, amma na wannan shekara zai fi sauran da aka gudanmar a shekarun baya.

Salima Jioraj wadda ita ce ke jagorantar shirya wannan babban baje kolita bayyana cewa, za a samu halartar kamfanonin abincin Halal fiye da 100 a wannan baje koli, kuma za a ware dakuna kimanin 200 na kayayyakin abincin Halal iri-iri, wanda ake sa ran fiye da mutane dubu 35 za su zo wurin domin duba abubuwan da musulmi suke amfani da su a matsayin abincin Halal.

Wannan taron baje koli dai yana samun halartar musulmi da ma wadanda ba musulmi ba daga sassa daban-daban na kasar Canada, kamar yadda yadda kumka wasu kamfanoni da suke samar da irin wannan abinci sukan zo su nuna abubuwan da suke samarwa.

A kan yi cinikin abincin Halal a kasar Canada da ya kai na dala biliyan guda a kowace shekara, sakamakon karuwar musulmi da ake samu a kasar da suke yin amfani da shi, kididdiga dai ta nuna cewa adadin musulmin Canada zai ninka sau uku daga nan zuwa shekara ta 2031.

3615752


captcha