IQNA

Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Gargadi Dangane Da Karuwar Kyamar Musulmi

23:54 - July 10, 2017
Lambar Labari: 3481687
Bangaren kasa da kasa, a cikin wani bayani da majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar ta yi gargadi dangane da yadda kyamar musulmi ke ci gaba da karuwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na IINA cewa, jami’an ‘yan sandan kasar Birtaniya sun fitar da wani rahoto da ke tabbatar da karuwar kin jinin musulmi a yankuna daban-daban na kasar ta Birtaniya , tun bayan kaddamar da harin da kungiyar ‘yan ta’addan ISIS ta yi a biranan London da kuma Manchester.

A nata bangaren majalisar musulmin kasar ta Birtaniya ta fitar da nata jawabin da ke cewa, tun bayan kai hare-haren na London da Manchester, kyamar musuli da cin zarafinsu da kuma yin barazana a kansu ya ninka sau biyar.

Harun Khan babban sakataren majalisar musulmin Birtaniya ya bayyana cewa, wannan lamarui ne mai matukar hadari, domin kuwa a halin yanzu musulmi a kasar Birtaniya suna fuskantar barazana daga wasu masu tsanannin kiyya da addinin muslnci, bisa hujjar cewa musulmi ne suke kaddamar da hare-haren ta’addanci.

Harun Khan ya bayar da misalign harin da aka kai a kan musulmi a Finsbury Park bayan kammala salla, tare da kasha wani da kuma jikkata wasu, ya ce babu wani dalili da masu kai irin wadannan hare-hare kan musulmi za su fake da su, domin kuwa su kansu musulmin suna daga cikin wadnada hare-haren ta’addancin ke rutsawa da su, kuma babu wani musulmi na kwarai da zai taba amincewa da abin da ‘yan ta’adda suke yi da sunan addinin muslunci ko sunnar manzon Allah.

Daga karshe ya kirayi gwamnatin Birtanita da kuma jami’an tsaro da suka fitar da wannan rahoto a kan cewa su sauke nauyin da ya ratay a kansu na kare rayukan msulmi da dukiyoyinsu da kuma mutuncinsu.

3617430


captcha