IQNA

Kenya: Za A Dauki Malaman Kwantaragi Domin Hana Yaduwar Tsatsauran Ra'ayin Addini

22:01 - July 11, 2017
Lambar Labari: 3481691
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Kenya za ta fara aiwatar dacwani shiri na daukar malaman makarantu domin hanay yaduwar tsatsauran ra'ayin addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da a'aikatar ilimi ta kasar Kenya ta fitar, ta bayyana cewa za a fara gudanar da shirin daukar malaman kwantaragi da za su taimaka wajen wayar da kan dalibai a makarantun sakandare kan lamarin addini da kuma kyawawan dabi'u na zamantakewa.

Bayanin ya ce wannan zai hada da koyar da kyawawan dabi'u na addinai, musamman kiristanci da muslunci, bisa la'akari da cewa akasarin mutanen kasar kiristoci ne, yayin da musulmi kuma suke biye musu wajen yawa a kasar.

Babbar manufar wanann shiri dai ita ce yada zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al'umma duk kuwa da irin banbancin addini ko al'adu da ke tsakaninsu, tare da hana yaduwar tsatsauran ra'ayin addini wand aka iya kai matasa ga aikata barna ko aikin ta'addanci da sunan addini.

Ma'aikatar ilimi ta kasar Kenya ta ce yanzu haka akwai malamai 200 da aka fara dauka wadanda za su fara samun horo kan manufar shirin, kafin daga bisani kuma za a ci gaba da kara adadin malaman da za su hada da msuulmi da kuma kiristoci, kuma za a fara aiwatar da shirin ne a cikin shekara ta 2018 mai kamawa.

3617630


captcha