IQNA

Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka A Kan Saudiya Kan Kisan 'yan Kasar

23:53 - July 13, 2017
Lambar Labari: 3481695
Bangaren ksa da kasa, Amnesty Internatinal ta yi kakkausar a kan masarautar 'ya'yan Saud da ke rike da madafun iko a kasar Saudiyya, dangane da kisan fararen hula masu nuna adawa da salon mulkinsu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta fitar a jiya, ta bayyana cewa masarautar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa har lahira akan wasu fararen hula guda 4 da take tsare da su, dukkaninsu 'yan yankin Qatif ne na mabiya mazhabar shi'a da ke gabashin kasar, bisa tuhumarsu da ayyukan ta'addanci.

Kungiyar Amnesty Int. ta ce bisa ga bincikenta babban laifin da wadannan mutane suka aikata ga gwamnatin Saudiyya shi ne, sun shiga cikin zanga-zangar nunaadawa da salon mulkin kasar ne da suke ganin yana tauye musu hakkokinsua matsayinsu na 'yan kasa,a kan haka gwamnatin Saudiyya ta harbe su a ranar Talata da ta gabata.

Al'ummar yankunan gabashin saudiyya wadanda mabiya mazhabar shi'a ne, suna kokawa dangane da yadda aka mayar da su saniyar ware da kuma haramta musu dukkanin hakkokinsu na 'yan kasa a kasarsu, tare da cewa dukkanin arzikin man fetur da iskar gas da tattalin arzikin kasar ya dogara a kansa, daga yankunansu ake hako su.

3618492


captcha