IQNA

Amnesty International Ta Soki Masarautar Bahrain

21:36 - September 07, 2017
Lambar Labari: 3481874
Bangaren kasa da kasa, hukumar kare hakin bil-adama ta Amnesty International ta soki kasar Bahrain game da rashin aiki da alkawarin da ta dauka na mutunta hakin bil-adama.

cikin wani rahoto da hukumar kare hakin bil-adama ta Amnesty International ta fitar a wannan Alkhamis, ta ce kasar Bahrain ba wai kawai ba ta yi aiki da alakawarin da ta dauka ba, saidai ta ci gaba da kame tare da azabtar da 'yan adawarta na siyasa, kuma ya zama wajibi birnin na Manama ba tare da gindaya wani sharadi ba ya sako dukkanin fursunonin siyasar da yake tsare da su.

Har ila yau hukumar kare hakin bil-adama ta Amnesty International ta bukaci kasar Bahrain din da kadda ta zartar da hukuncin da majalisar dokokin kasar ta dauka na rusa manyan jam'iyu biyu na 'yan adawar kasar.

Tun daga watan Fabrairu na shekarar dubu biyu da goma sha daya ne al'ummar kasar Bahrain ta fara gudanar da zanga-zangar neman 'yancin siyasa a kasar, duk da irin amfani da karfi da masarautar Bahrain ke yi, har yanzu ta kasa murkushe al'ummar kasar.

Yanzu haka dai akwai mutane fiye da dubu daya da suke tsarea hanun mahkuntan kasar saboda dalilai na siyasa na bannabcin akida, daga cikin su kuwa har da mata da kuma kananan yara, wanda hakan yak e kara tabbatar da cewa kasar bata da niyar yin sassauci daga bin tsarinta na  kama karya.

3639573


captcha