IQNA

An Kashe Musulmi 7 A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

16:56 - November 14, 2017
Lambar Labari: 3482100
Bangaren kasa da kasa, Fada tsakanin masulmi da kuma kiristoci a wata unguwa a birnin Bangi babban birnin kasar afrika ta tsakiya ya lashe rayukana musulmi akalla.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, da farko wasu mahaya babura sun jefa girneti a cikin wani shagon shan koffi a unguwan da musulmi suka fi yawa a birnin, sannan daga baya suka bude wuta kan wani bikin da ake yi a unguwar wanda ya kai ga mutuwar musulmi 7 da kuma raunata wasu.

Majiyar kungiyar Seleke ta musulmi ta tabbatar da wannan labarin haka ma majiyar sojojin tabbatar da zaman lafiya na MDD a cikin birnin ta ce hakan ya faru kuma ana zaton kungiyar anti balaka ta kiristoci a cikin birnin ne suka kai hare haren na jiya Litinin.

Wannan dai bas hi ne karon da majalisar dinkin duniya take bayar da bayanai kan kisan gillar da ake yi wa msuulmi ba, duk da cewa babu wani abu da aka dauka domin dakatar da hakan da kuma kare rayukan musulmi.

3663178


captcha