IQNA

Musulmi Sun Buga Katuka Masu Taya Kiristoci Murnar Kirsimati A London

23:48 - December 26, 2017
Lambar Labari: 3482238
Bangaren kasa da kasa, daliban jami’a musulmi ‘yan asalin kasar Iran mazauna birnin London sun yi katukan taya kiristoci murnar kirsimati.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar daliban jami’a musulmi ‘yan asalin kasar Iran mazauna birnin London na kasar Birtaniya ta buga katukan taya kiristoci murnar kirsimati wadanda suke dauke da ayaoyin kur’ani.

Bayanin ya ce a cikin wannan katuna an yi saka ayoyin kur’ani da suke yin magana kan annabi Isa (AS) da kuma bayyana matsayinsa mai girma  a cikin adinin muslunci.

Wadannan dalibai sun rika raba wadannan katuka ga mabiya addinin kirista  acikin birnin London tare da taya su murnar zagayowar lokacin haihuwar annabi Isa Almasihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi.

Babbar manufar yin hakan dai ita e kara kusanto da fahimtar juna tsakanin musulmi da kiristoci domin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin mabiya addinan guda biyu.

3676567

آیات قرآن؛ زینت‌بخش کارت تبریک‌‌های کریسمس در لندن+عکس

 

آیات قرآن؛ زینت‌بخش کارت تبریک‌‌های کریسمس در لندن+عکس

 

آیات قرآن؛ زینت‌بخش کارت تبریک‌‌های کریسمس در لندن+عکس

 

آیات قرآن؛ زینت‌بخش کارت تبریک‌‌های کریسمس در لندن+عکس

 

 

 

 

 

captcha