IQNA

Daruruwan Amurkawa Sun Gudanar Zangar-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Palastinu

23:58 - June 08, 2018
Lambar Labari: 3482740
Bangaren kasa da kasa, daruruwan Amurka ne suka gudanar da jerin gwanon nuna goyon bayan ga al’umma Palastnie mazauna zirin Gaza.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa daruruwan Amurka ne suka gudanar da jerin gwanon nuna goyon bayan ga al’umma Palastnie mazauna zirin Gaza dangane da kisan kiyashin da yahudawa sra’ila key i a kansu.

An gudanar da wannan jerin gwano a manyan birana daban-daban na kasa Amurka domin nuna wa gwamnatin kasar cewa goyon bayan kisan kiyashi kan Palastinawa da take ba abu ne da al’ummar kasar suka amince da shi ba.

Wannan zanga-zanga ta hada jama’ daban-daban da suka hada da musulmin Amurka, da kuma sauran jama’a wadanda ba musulmi ba, da suka hada da masu rajin kare hakkin bil adaa da masu yaki da nuna wariya ga wani jinsi na dan adam.

Ko a kwanakin baya ma wadannan kungiyoyin sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana birnin quds a matsayin babban birnin Isra’ila da Trump yay i.

3720638

 

 

 

 

captcha