Kamfanin dillancin labaran labaran iqna ya habarta cewa, a yau an gudanar da tarukan ranar Ghadir a birnin Sa’ada da kuma wasu birane na kasar Yemen a yau tare da halartar dubban daruruwan musulmi.
Wannan taro na daga cikin taruka na tarihi da al’ummar Yemen suke gudanarwa a kowace shekara, musamman ma ayankunan rewacin kasar.
Akwai a’adu da dama da suke da su da suke gudanarwa awannan rana mai albarka da matsayi a cikin addinin muslunci, ranar cikar addini da kuma bayanai na karshe da manzon Allah ya yi wa al’ummar musulmi kan makomarsu a bayansa.