IQNA

An Bude Cibiyar Siddiqa Tahira A Kasar Ghana

15:33 - December 02, 2018
Lambar Labari: 3483172
Bangaren kasa da kasa, an bude babbar cibiyar musulunci ta Siddiqa Tahira ta mabiya Ahlul bait (AS) a garin Komasi na kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka an bude babbar cibiyar musulunci ta Siddiqa Tahira ta mabiya Ahlul bait (AS) a garin Komasi na kasar Ghana tare da halartar Sayyid Moradi, wakilin shugaban ofishin jagoran juyin juya halin musulunci.

Wannan taro ya samu halartar malamai da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar Ghana, kamar yadda kuma wasu daga cikin ‘yan kasashen ketare mazauna kasar suka halrci wurin taron, musamman daga kasashen larabawa.

Sayyid Moeradi ya isar da sakon ofishin jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a wurin taron, inda ya bayyana cewa, jagora yana kallon al’ummar muuslmi na Afrika da kuma yammacin Afrika  a matsayin mutane masu karfin imani da nuna soyayya ga manzon Allah da iyalan gidansa.

Shi ma a nasa bangaren Muhammad darul Hikma shugaban cibiyar yada sakon ahlul bait a Ghana ya gabatar da nasa bayanin, inda ya yaba da irin kokarin da mutanen kasar suke nunawa wajen kare martabar manzon Allah da ahlult da kuma nuna musu soyayya.

3768301

 

 

captcha