IQNA

Nabih Birri Ya Gana Da Ayatollah Sistani

23:29 - April 02, 2019
Lambar Labari: 3483510
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Birri yana gudanar da wata ziyara ta musammana kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Talabijin ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, shugaban mjalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Birri yana gudanar da wata ziyara a kasar Iraki, inda yake ganawa da manyan jami'an gwamnati da malamai na kasar.

Rahotin ya ce, a yayin ziyarar tasa shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya gana da takwaransa  na Iraki, kamar yadda ya gana da Firayi ministan kasar, kamar yadad kuma yake da shirin ganawa da shugaban kasar da wasu manyan jami'ai.

A jiya Nabih Birri ya gana da babban malamin addinin muslucni na kasar ta Iraki Ayatollah Sistani, inda suka tattauna muhimamn batutuwa da suka yankin gabas ta tsakiya, da kuma wajabcin samun sulhu da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin dukkanin al'ummomin yankin.

Babbar manufar ziyarar dai ita ce tattauna yadda kasahen Lebanon da Iraki za su kara hada karfi da karfe domin tunkarar barazanar ta'addanci, da kuma kara karfafa alakoki diflomasiyya a tsakaninsu.

3800623

 

captcha