Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron girmama wasu dalibai 135 mahardata kur’ani a kasar Masar a lardin Bahrul Ahmar.
Rahoton ya c dukkanin wadannan maardata sun fito daga lardin an bahrul Ahmar inda mahukunta ajahar suka dauki nauyin bayan da kyautuka na musamman a gare su.
Babbar manufar hakan dai ita ce karfafa dalibai da matasa kan lamarin kur’ani mai tsarki a fadin kasar ta Masar.
Haka nan kuma a daya bangaren an girmama iyaye mata abin koyi na shekara ta 2019, saboda tarbiyantar da yaransu kan kur’ani.