Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau Chandana Wickramaratne babban sufeton ‘yan sanda na kasar Sri Lanka ya bayyana cewa, sun samu nasarar kame ko kuma kashe dukkanin wadanda suke da hannu a hare-haren ta’addancin da aka kai a kasar a ranar 21 ga watan Afirilun da ya gabata.
Ya ce an kai samame a maboyar ‘yan ta’addan a wurare daban-daban, kuma an samu tarin makamai da abubuwan harhada bama-bamai da wasu abubuwa masu tarwatsewa.
Haka nan kuma ya kara da cewa, an dauki kwararan matakan tsaro a dukkanin wurare taruwar jama’a, musamman a makarantu, inda ‘yan ta’addan ke barazanar za su kai hare-hare.
A ranar 221 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai aka kai hare-haren ta’addanci, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 257, da kuma jikkatar wasu 500 na daban.