Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ta'addancin ne akan wata majami'ar mabiya addinin kirista a kasar Burkina Faso.
Rahoton ya ce maharan sun kai harin ne a lokacin da mabiya addinin kirista suke gudanar da iabada a cikin majami'ar tasua jiya Lahadi, kuma an kashe babban malamin majami'ar tare da wasu mutane 6a wurin.
Haka nan kuam rahoton ya kara da cewa 'yan bindigar sun bude wuta akan wuraren jama'a da hakan ya hada da wani babban shagon sayar da magunguna, inda suka tarwatsa mutane, kuma suka banka wuta akan wata motar daukar marassa lafiya.
jami'an tsaro sun ce adadin mutanen da suka kai harin ya kai mahara 20 zuwa 30.