IQNA

23:58 - June 07, 2019
Lambar Labari: 3483719
Bangaren kasa da kasa, a yau Juma’a aka bude masallaci na farko a babban birnin Athen na kasar Girka

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Greek City Times ta bayar da rahoton cewa, a yau Juma’a an bude masallaci na farko a birnin Athen babban birnin daya daga cikin manyan kasashen turai da babu masallaci a cikinsa.

Taron bude masallacin na farkoa  birnin Athen ya samu halartar manyan jami’ai da suka hada da Costas Garoglo ministan ilimi da kuma kula da harkokin addinai a kasar Girka, da kuma wasu daga cikin masana da malaman addini.

Tun bayan kawo karshen ikon daular Usmaniya a kasar Girka aka rusa dukkanin masallatan da suke cikin birnin Athen, kuma tun daga lokacin ba  akara gina wani masalalci a birnin ba.

Gina wannan masallaci dai ya fuskanci adawa daga bangarori daban-daban na ‘yan siyasa a kasar Girka, amma daga karshe dai gwamnatin kasar ta amince da gina shi da kuma bude shi bisa wasu sharudda.

Daga cikin sharuddan da aka gindaya har da gina masallacin ba tare da hasumiya ba, kamar yadda kuma ba a bayar da izinin a yi amfani da lasifika a masallacin ba, kuma fadin masallacin zai iya daukar masallata maza 300 ne kawai, sai kuma mata 50, kuma za a rika bude masallacin n sa’a guda kafin lokacin salla, da zaran an gama salla kuma za a rufe shi, in banda cikin watan Ramadan inda masallacin zai iya kasance bude a kowane lokaci.

3817450

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hasumiya ، kasancewa ، Girka ، masallaci ، Athen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: