IQNA

22:10 - June 08, 2019
Lambar Labari: 3483721
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Saudiyya ta kudiri aniyar sare kan wani karamin yaro wanda ta kame tun shekaru biyar wanda yanzu yake da shekaru 18 a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, cibiyar kare hakkokin fursunonin kasar Saudiyya ta sanar da cewa, masarautar saudiyya na shirin sare kan wani yaro da take tsare da shi tun dubu da sha hudu.

A cikin shafinta na yanar gizo, cibiyar ta bayyana cewa, babban mai shigar da kara na masarautar Saudiyya, ya bukaci da a zartar da hukuncin kisa kan Murtaja Qarisis, wanda aka kama shi yana da shekaru 13 da haihuwa, bisa tuhumarsa da cewa ya shiga jerin gwano agabashin Saudiyya, domin nuna rashin amincewa da salon mulkin mulukiya na masarautar kasar, da kuma neman hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu an ‘yan kasa.

Rahoton ya kara da cewa, jami’an tsaron Saudiyya sun kame Murtaja ne alokacin da yake kan hanyarsa ta yin tafiya tare da mahaifansa zuwa kasar Barain, kuma an azabtar da shi acikin kurkuku, tare da tilasta shi sanya hannua kan wasu tuhumce-tuhumce da aka kirakiraa kansa.

Yanzu haka dai akwai adadi mai yawa na masu fafutuka da suke tsare agidajen kason saudiyya, wadanda a kowane lokaci za a iya sare kawunnansu, sakamon ra’ayinsu na siyasa da kuma kare hakkokin ‘yan adam da suke yi a kasar.

 

3817726

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: