Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Ptra na kasar Jordan cewa, Abdulnasir Abulbasar ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar ya bayyana cewa, daga yanzu idan za a dauki limamai a masallataia kasar, za a fifita mahardata kur’ania kan waunsu.
Ya ci gaba da cewa a halin aynzu ma’aikatarsa tana da wani sharia abnagaren ayyukan kur’ani, inda shirin yake da nufin kara yawan adadin mahardata kur’ani da ake ad su a kasar.
Abdulnasir Abulbasal ya ce, a kowace shekara ana yayae mahardata kur’ani kimanin dubu biyu a kasar, wanda adadin na bukatar a kara shi.
Dangane da limancin masallatai ya ce, akwai karancin liammai wadana suka hardace kur’ani a kasar.
Saboda haka a nan gaba a cewarsa, limamanci zai zama aikin wadanda suka hardace kur’ani ne koda wani bangarensa ne kamar rabi ko kusa da haka, baya ga sauran ilmomin da ake bukata.
Yahya Saud wakilin makarantar yan mata ta Muhammad Mahmud Saud ya bayyana cewa, suna gudanar da sare-tsarensu cikin nasara, inda suke yaye daruruwan mahardata a kowace shekara.