Kamfanin dillancin labaran IQNA, shugaba Hassan Rauhani ya yaba wa matakin da al’umma ta dauka na ware kansu daga cikin masu tayar da tarzoma wadanda suke samun umarni daga makiyan kasar. Su ne suka kashe jami’an tsaro, suka kona kayayyakin gwamnati da na al’umma.
Yayin da yake gabatar da jawabi a taron ministocinsa da ya gudana a wannan Laraba, shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa al’ummar kasar ta fito ne daga wata jarrabawa ta musamman wacce ta zama tarihi.
Rouhani ya tabbatar da cewa al’ummar ta fahimci cewa manufarta ita ce tabbatar cewa kasar ta wadatu daga kasashen ketare musaman ma a bangaren makamashi, ta yadda za ta kasance mai dogaro da kanta don biyan bukatun mutanen kasarta.
A yayin da yake ishara kan zanga-zangar da ta wakana a baya-bayan nan shugaba Rouhani ya ce akwai iyalai kimanin miliyan 18 dake rayuwa cikin talauci, don haka za a yi amfani da kudade karin farashin makamashi don taimaka musu.