IQNA

Hizbullah Ta Kakkabo Jirgin Leken Asiri Na Isra'ila A Kudancin Lebanon

18:43 - September 30, 2021
Lambar Labari: 3486369
Tehran (IQNA) kungiyar Hizbullah ta kakkabo jirgin leken asiri na Isra'ila a kudancin kasar Lebanon.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta kakkabo jirgin leken asiri na Isra'ila a kudancin kasar Lebanon a yau Alhamis.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce jirgin yana shawagi ne a kan iyakokin Falastinu da Isra'ila ta mamaye da kuma iyayokin Lebanon, daga lokacin kuma aka ra bayanan da jirgin ke aikowa, wanda hakan yasa aka shiga bincike.

Daga bisanin Isra'ila ta tabbatar da cewa Hizbullah ce ta batar da jirgin, kuma kungiyar ta Hizbullah ta yi amfani da wasu na'urori ne na musamman wajen sauko da jirgin kasa ba tare da ta tarwatsa shi ba, ta yadda za ata iya samun dukkanin bayanan da jirgin yake dauke da su.

Gwamnatin yahudawan Isra'ila ta bayyana cewa, samun wannan fasaha da ci gaba da kungiyar Hizbullah ta yi, hakan da cewa yana matukar hatsari ga Isra'ila.

 

4001465

captcha