IQNA

Kasashen Tarayyar Turai Sun Kirayi Isra'ila Da Ta Daina Gina Matsugunnan Yahudawa A Yankunan Falastinawa

15:44 - October 29, 2021
Lambar Labari: 3486488
Tehran (IQNA) kasashen kungiyar tarayyar turai sun kirayi Isra'ila da ta dakatar da gina matsunnan yahudawa a ckin yankun an Falastinawa.

A ranar laraba ce babban kwamitin tsare-tsare na Isra’ila ya fitar da amincewarsa ta karshe game da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa yan share wuri zauna guda 1800 da kuma Karin wasu guda 1,344 da kwamitin soji dake kula da harkokin fararen hula a yankunan falasdinawa.

A wata sanarwar hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen Belgium da Denmark da Finland da Jamus Italiya Netherland, Norway, Poland da Sweden suka fitar a yau Alhamis sun bayyana adawar su a fili gami da ci gaba da gina sabbin matsugunnan yahudawa da Isra’ial take yi a yankunaa falasdinawa.

Har'ila yau sun bukaci Israila da ta dakatar da shirinta na sake gina matsugunan yahudawa guda 3000 a gabar yammacin kogin jodan.da ma dukkan yankuna palasdinawa da ta mamaye.

A na ta bangaren kungiyar Hamas ta yi tir da wannan shirin na gina matsaugunan yahudawa da Isra’ila ke yi da sauran gwamnatocin Isra’ila da suka shude suka bi, kana ta bayyana shi a matsayin babban laifin yaki.

 

4008734

 

captcha