IQNA

Dubban Falasdinawa ne suka halarci sallar asuba a masallacin Al-Aqsa

17:08 - March 11, 2022
Lambar Labari: 3487036
Tehran (IQNA) Dubban Falasdinawa ne suka yi tattaki zuwa masallacin Al-Aqsa inda suka halarci sallar asuba a cikin masallacin mai alfarma.

Dubban Falasdinawa mazauna birnin Kudus da yankunan 48 da aka mamaye da gabar yammacin kogin Jordan musamman mata masu yawan gaske ne suka isa masallacin Al-Aqsa a yau duk da rashin kyawun yanayi da tsaurara matakan tsaro na sojojin yahudawan sahyoniya.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan yahudawan sahyuniya suka hana Falasdinawa da dama daga gabar yammacin kogin Jordan shiga birnin Kudus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran Falasdinu cewa, dubban Falasdinawa mazauna birnin Kafr Qasim ne suka yi jerin gwano a cikin ayari zuwa masallacin Al-Aqsa daga cikin yankuna 48 da aka mamaye.

Har ila yau, wani rahoton ya bayyana cewa 'yan mamaya na yahudawan sahyoniya sun kai hari a Jenin, Tulkarm da Hebron, tare da kai hari kan gidaje da dama.

Sojojin yahudawan sun murkushe Falasdinawa a lokacin hare-haren, lamarin da ya kai ga gwabza fada tsakanin Falasdinawa da mayakan Sahyoniyawa.

Ya kamata a lura cewa sojojin yahudawan sun kai hari a yammacin kogin Jordan a kowace rana tare da danne Falasdinawa.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4042034

captcha