IQNA

Ayatollah Khamenei: Matukar Dai Yahudawa Suna Mamaye Da Masallacin Al-aqsa To Kowace Rana ranar Quds Ce

17:37 - April 29, 2022
Lambar Labari: 3487231
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya tabbatar da cewa irin dimbin jama'a da suka halarci tarukan ranar Qudus ta duniya a yau, wani mataki ne na kare birnin Kudus.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wanda gidajen talabijin suka watsa kan ranar Qudus ta duniya cewa, tsayin daka na Palastinawa yana samun karfinsa ne daga irin wadannan taruka masu albarka.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa matukar dai 'yan mamaya yahudawan sahyoniya sun mamaye birnin Kudus, to dukkanin ranakun shekara ana daukar su a matsayin ranar Qudus ta duniya, yana mai nuni da cewa matasan da suke gudanar da ayyukan sadaukarwa sun zama garkuwa ga Kudus.

Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa, a yau muna ganin Amurka tana fama da shan kashi a fagagen siyasa, da kuma yadda yahudawan sahyoniya suke kai komo  a fagen siyasa da na soja cikin sarkakiya na matsaloli.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa yunkurin jihadin da Palastinawa suka yi a yankunan arewaci da kudancin kasar a shekara ta 1948 yana nuni da cewa dukkanin Palastinu ta koma wata maraya ta gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce taken da masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Turai suke ya tabbata cewa ba gaskiya ba ne, domin suna yin watsi da laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa kan yara da mata.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa karfin juriyar da suke da shi zai kawar da  'yan ta'addar sahyoniyawan ta hanyar jihadin su.

 

4053497

 

captcha